Jump to content

Cibiyar Abul-warakat

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

CIBIYAR ABUL-WARAKAT (ABUL-WARAKAT FOUNDATION / مؤسسة أبي الورقات)

Cibiya ce da kwararren marubuci, mawaki kuma malami Binyamin Zakari Hamisu da ake wa lakabi da Abul-warakat ya samar a jahar Kano, cikin jamhuriyyar Najeriya, cikin shekarar 2024.[1]

MANUFOFI :

An samar da tubalin wannan cibiya ne bisa cim ma manufofi masu zuwa :

- Bayar da horo da dabarun kwarewar a fannonin neman kudi da kasuwanci, domin samun sana'o'in dogaro da kai, musamman a shafukan sadarwa na zamani.

- Cibiyar wani zaure ne na kwararru a rubutun fim (scrift writing), wanda suke aikin samar da ingantattun labaran dim, masu gajeren zango da masu dogon zango, wadanda za su ginu bisa kula da harshe da nagartattun al'adun Hausawa da addininsu. Bugu da kari, a wannan bangaren, cibiyar ta fara kokarin samar da fim din Hausawa na farko a Najeriya cikin harshen Larabci, mai taken Alfakaru Wal Gina الفقر والغنى  wato Talauci da Wadata.

- Har ila yau, fassara wani jigo ne a tafiyar da wannan cibiya, wadda ta sa dambar fassara cikin yarurrukan Ingilishi, Larabci zuwa Hausa.

- Koyar da darussa ta wayar hannu (Online), inda cibiyar ta fara samar da ajujuwa a shafukan sadarwar zamani, domin koyar da yarurrukan Arabiyya da Ingilishi, da ma iliman na'ura mai kwakwalwa da fasahar zamani.

- Samar da ingantattun litattafai da wakoki na ilmantarwa, fadakarwa, nishadantarwa da siyasa.

- Samar da litattafai da kuma buga su.

- Gabatar da ayyukan taimaki da tallafa wa al'umma, d.s.

A jawabinsa ranar samar da cibiyar, ranar Litinin 1 ga watan Ranadhan na shekarar 1445, wanda ya yi daidai da 11/3/2024, Shugaban cibiyar Binyamin Zakari Hamisu, ya bayyana wadannan manufofi, ya kara da cewa "Duk mutumin da yake tunanin yau zai mutu ko gobe zai mutu, ba shi da lokacin bata lokaci domin ya nemi suna ko ya nemi daukaka... Ba cibiya ce ta daukaka Kai ba, cibiya ce ta daukaka aiki".

  1. https://youtu.be/-uZPRLMeNlk?si=eeHdBblCyD2lszW9