Jump to content

Ciyayya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
hoton kalar abinci da ake ciyayya
Ciyaya

Ciyayya Wata dabi'a  ce wadda Bahaushe ya gaje ta tun iyaye da kakanni, amma yanzu ta dace. A zamanin da, kusan dukkan magidanci yakan fito da abinci kofar gida, don su hadu su ci abinci a kofar gida.

A inda shi ma makwabcinsa zai fito da nasa abinci, don su hadu su ci abincin nan tare. Wannan dabi’a ba karamin taimako take yi ba, saboda tana kyautata zamantakewar makwabtaka, a inda aka zama tamkar dan uwa na jini. Haka kuma yana taimakon wanda bai samu yin girki ba, ko kuma mara mata (Tuzuru, ko gwauro ko bako), sannan da almajirai wani lokaci har da mahaukata kai har da dabbobi.[1]

Kwaram sai zamani yayi fatali ko jifar matacciyar mage da wannan dabi’a. a yau mafi yawa kowa yana cin abincinsa ne a cikin gida ko daki a inda ake ajiye masa a kula da shi kadai. A yanzu zamani ya koya mana ci naka in ci nawa ba rowa bane, to amma Bahaushe yace mugun zama ne.[2][3]