Jaridar Complete Sports
Appearance
(an turo daga Complete Sports)
| Bayanai | |
|---|---|
| Iri |
sports newspaper (en) |
| Ƙasa | Najeriya |
| Harshen amfani | Turanci |
| Mulki | |
| Hedkwata | jahar Legas |
| Tarihi | |
| Ƙirƙira | Disamba 1995 |
Complete Sports jaridar wasanni ce ta kasa kullum kuma tana da hedkwata a Isolo, karamar hukumar jihar Legas. An fara buga ta ne a shekarar 1995 a matsayin babbar jaridar Complete Communications Limited kuma ta kasance daya daga cikin jaridun da aka fi karantawa a Najeriya.[1] Jaridar ta fi mayar da hankali akan yan wasanni Najeriya musamman ’yan kwallon kafa na Najeriya.
Jaridar Complete Sport ta samu karbuwa a sassan Najeriya da wasu sassa na jamhuriyar Benin da Kamaru don haka ta zamo jaridar da ta zagaye yankuna yammacin Afirka.[2]