Jump to content

Dariya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
dariya
facial expression (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na smiling or laughing (en) Fassara da animal vocalization (en) Fassara
Has cause (en) Fassara amusement (en) Fassara
Yaro yana dariya
Sautin Muryar Mace tana dariya

Dariya wata abu ce da take faruwa a jikin dan Adam kuma tana fitowa ne da taimakon wasu sassa na jiki kuma tana fitowa wajene a fili duk sanda akayita. Dariya takan faru a wasu lokuta yayin da aka yi maka cakulkuli ko kuma daga labarai masu ban nishadi, bidiyoyi da kuma tunani.

A wasu lokutan, dariya takan fito yayin da wani abu ya faru musamman a cikin yanayin farin ciki kamar shagali, murna ko hutawa. A wasu lokutan, dariya tana faruwa a wasu lokuta da dama kamar yanayin tozarci, yanayin wulakanci, da kuma mamaki da rudani. Dariya tana faruwa da jinsi kala kala walau mace ce ko kuma namiji. Haka zalika dariya tana kamawa a lokuta da dama kamar wajan karatu, shekaru, da kuma likaci na nishadi. Dadin dadawa, anayin dariya wajan wasanni kamar wasan kaukawa, wasan dara sa kuma wasan kati.

Dariya tana cikin dabu'u na mutum wadda take a kwalwar mutun saidai ana fiddata da baki ne tana taimaka ma mutun wajan nuna farin cikinsa a wajan tattaunawa, kuma alamace da mutun keyi idan ana a cikin taro

Fannin lafiya

Hadi tsakanin dariya da kuma lafiya alakace mar misaltuwa, a wasu lokuta da dama dariyar takan zama illa idan ta cika yawa a jikin dan adam, kuma tana taimakama jiki domin karin lafiya a jiki. Dariya tana taimakawa wajan shige da fice na jini kuma takan taimaka wajan fidda nitric oxide

Tattaunawa

Adadin dalibai da suka karanci hanyoyin tattaunawa da kuma ittifaki sun ajiye bayanai cewa aikin da dariya keyi a wurare da dama, kamar karamar tattaunawa, tattaunawa ta neman aiki, taro da sauran tattaunawa. Anyi ajiye dukkanin abinda y faru a tattaunawar. Bincike ya nuna cewa dariya bata zuwa haka nan siddan ragadan ba tare da faruwar wani abun ba. Kuma sun gano cewa a koda yaushe kwalwar mutun takan iya tuno mashi da wani abu da zaisa kwatsam aga yayi dariya.

Stearns, Frederic Rudolph (1972). Laughing: Physiology, Pathology, Psychology, Pathopsychology and Development. Springfield, Ill., Thomas. pp. 59–65. ISBN 978-0398024208.

Shultz, T. R.; Horibe, F. (1974). "Development of the appreciation of verbal jokes". Developmental Psychology. 10: 13–20. doi:10.1037/h00355

Olmwake, Louise (1937). "A study of sense of humor: Its relation to sex, age and personal characteristics". Journal of Applied Psychology. 45 (6): 688–704. doi:10.1037/h0055199.