Jump to content

Dashishi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Dashishi abincin gargajiya ne da ke kara lafiya da kuzari tare da gina jiki, ga shi kuma da dadin gaske.

Kayan da ake bukata:[gyara sashe | gyara masomin]

  • Alkama kofi 8
  • Mai kofi 1
  • Gishiri kadan
  • Ruwa

Yadda ake yi:[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ki sami alkama ki tsince ta sai a surfeta a cire dusar.
  2. A wanke ta, a bari ta bushe, sai a nika a barzo ta amma kada ta yi gari sosai.
  3. A zuba ruwa a tsame ta yadda barjin zai yi laushi idan an turara shi, sai a tsame.
  4. A sami madanbaci a turara shi, har sai ya fara cuccurewa,
  5. Daga nan sai a zuba mai da gishiri a juya sosai amma a sauke.
  6. Sai a sa mai yadda zai warware, a kara mayarwa shi kan wuta.
  7. Idan ya yi za a ji yana kamshi, sai ci.

Ana ci da miyar taushe ko miyar ganye ko duk miyar da ake so.