Jump to content

David Edevbie

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
David Edevbie
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

David Edevbie dan siyasan Najeriya ne kuma tsohon dan takarar jam'iyyar People's Democratic Party, (PDP) a zaben gwamnan Najeriya a 2023 a jihar Delta. Ya sha kaye a hannun Sheriff Oborevwori. Edevbie shi ne kwamishinan kudi da tsare-tsare na tattalin arziki a karkashin gwamnatin James Ibori tsakanin watan Yuni 1999 zuwa Satumba 2005. Ya kuma rike mukamin kwamishinan kudi a karkashin Gwamna Ifeanyi Okowa daga 2015 zuwa 2019. Edevbie ya zama Daraktan Kudi na kungiyar yakin neman zaben Umaru Musa Yar’Adua a shekarar 2006-2007 sannan ya zama babban sakataren shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua daga 2008 zuwa 2010. Na baya-bayan nan rawar da ya taka a rayuwar jama’a ita ce shugaban ma’aikatan gwamna Ifeanyi Okowa, wanda ya bar shi domin cimma burinsa na zama gwamnan jihar Delta.[1]

  1. Omon-Julius Onabu, "Court Removes Oborevwori, Installs Edevbie as Delta PDP Guber Candidate". thisdaylive.com. 30 July 2022. Retrieved 16 August 2022.