Jump to content

Denmark na shuka bishiyoyi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
iccen Denmark
iccen Denmark

Danmark na shuka bishiyoyi (Danish</link>) wani taron TV-telethon na Danish ne da aka gudanar a ranar Asabar 14 ga Satumba 2019 wanda ke da nufin tara kuɗaɗe don dasa sabbin bishiyoyi miliyan 1 a Denmark don zaburar da 'yan Danish suyi aikin sauyin yanayi. Ana dai kallon taron a matsayin telethon na farko a duniya don yaƙar matsalar yanayi.[1][2][3]

An watsa taron kai tsaye sama da awanni 2½ akan gidan talabijin na Danish TV2 kai tsaye daga hasumiya na gandun daji a Næstved wanda ke tsakiyar dajin. A yayin taron anyi wasannin kade-kade da shahararrun baki. Firayim Ministan Denmark Mette Frederiksen ta shuka daya daga cikin bishiyu na farko.[4] Telethon ya tara kudaden da suka isa shuka itatuwa 914,233, wanda ya kusa cimma burin da aka sa a gaba na itatuwa miliyan 1. An yanke shawarar cigaba da buɗe gidan yanar gizon bayar da gudummawa ta yanar gizo, kuma bayan makonni biyu an cimma burin itatuwa miliyan 1.[5]

Gidan talabijin na TV2 ne ya watsa taron wanda shine gidan talabijin na TV mafi girma mallakar gwamnati a Denmark, da nufin mayar da hankali kan sauyin yanayi, da kuma rawar da gandun daji da bishiyoyi ke takawa, wajen magance sauyin yanayi. Kamfanin samar da talbijin na Danish Tiki Media ne ya tsara wannan tsari, kuma furodusan ya bayyana fatan cewa taron zai bazu zuwa wasu kasashe, domin shiga cikin jama'a kan batun sauyin yanayi.[6][7]

Ƙungiyar Danish Growing Trees Network ta shuka bishiyoyi tare da haɗin gwiwar Danish Society for Nature Conservation.

  1. Denmark had the world's first-ever climate telethon | World Economic Forum
  2. Danes raise millions of euros in first-ever climate telethon | Deutsche Welle
  3. Danish project aims to plant 1m trees | The Guardian
  4. Danmark planter træer | TV2
  5. "Danmark planter mindst 1.000.001 træer| TV2". Archived from the original on 2019-10-15. Retrieved 2023-09-15.
  6. Nyt produktionsselskab stempler ind med klimaevent på TV 2 | Mediawatch
  7. Danish project aims to plant 1m trees | The Guardian