Dijatu Yerima Balla
Dijatu Yerima Balla (an haife ta ranar 30 ga watan Augusta, 1959). Ta kasance tsohuwar malamar makaranta ce, kuma mamallakiyar makarantar NADI, haka kuma tana da sassanin shakatawa na yara.[1]
Tarihin rayuwa da Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Dijatu Yerima Balla, an haife ta a karamar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.
Ta yi karatun Firamare a Gombi har zuwa aji biyu, a lokacin an yi Jihohin Arewa Maso Gabas, daga nan sai aiki ya kai mahaifinta Maiduguri sai suka koma can. Daga nan sai ta ci gaba da karatun firamare a Shehu Garbai a Borno. Shugaban makarantar Baturiya ce, wannan dalilin ya sanya suka samu ilimi mai inganci wanda babu ha’inci a ciki ko kadan. Daga nan sai ta yi karatun Sakandare a Kwalejin gwamnati ta ’yan mata da ke Maiduguri (G.G.S.S) da ta gama sai ta tafi Kwalejin Horar da Malamai ta Bauchi (Bauchi Teacher’s College) sai ta shiga fanin ilimi a gredi na biyu da niyyar idan ta gama karatun sai ta yi aure.
Da ta yi aure sai ta tafi Amurka inda ta yi karatun Diploma a koyon dinki bayan dawowarsu Nijeriya a lokacin Jihar Gongola ta koma Jihar Adamawa. A shekarar 1976, sai ta fara aikin koyarwa da shaidar karatu ta Grade I inda ta karantar a Kwalejin ’yan mata, GGSS Yola. Ta yi aiki har zuwa shekarar 1981, sannan ta koma kara karatu a Jami’ar Maiduguri inda ta karanci fannin ilimi da koyon harshen Turanci sannan ta kammala a shekarar 1985. Da ta gama a shekarar 1985, sai ta je bautar kasa ta dawo ne kuma sai ya kasance tana da sha’awar bude makaranta, domin wata malamarsu a sakandari mai koyar da su tarihi ta kitsa mata sha’awar bude makaranta, wannan dalilin ne ya sanya ta fara lalobo bakin zaren domin bude makarantarta na kashin kanta.
Kafa Makaranta
[gyara sashe | gyara masomin]Ta bude makarantar nata ne da dalibai biyu mafari a shekara ta 1988, inda ta samu karfin guiwa daga wata kawata ‘yar Ghana, lamarin da ya sanya suka samu zarafin kafa makarantar, inda a yanzu haka wannan makarantar nata ta doshi shekara talatin tana koyarwa da ilimi daban-daban. Makarantar wacce ta rada mata suna da NADI. Ta kuma samar da sunan Nadi din ne daga farkon sunan wata ’yar’uwanta Nafisa da ita Dijatu idan ka hada sunan za ka samu NADI.
Babban burinta dai a rayuwa bayan kafa makaranta sun hada da burin bude wajen wasa da shakatawa ga manyan gobe, tuni ta samar da wanna, sai kuma burinta na uku wanda yake kan kokarin samarwa yanzu haka shine cibiyar kiwon lafiya da ganin cewa sun samu kyakyawar kulawa a asibitocin gwamnati.[2]
Kalubale
[gyara sashe | gyara masomin]Gina makarantana na daya daga cikin babban kalubalen da ta fuskanta a rayuwarta. Domin a lokacin ba ta da isassun kudi sannan kawayenta ba su ba ta karfin gwiwa ba. Sai dai ta sanya wannan burin gina makaranta da kuma niyya. Ta sha gwagwarma na kusan shekara guda tana koyarwa ganin dalibai su fara mata tururuwa a makarantar nata, wanda yanzu haka wannan makarantar ya kai sunan a fadesa, rashin samun karfin guiwa ya kassarata, amma da ya ke ta sanya abun a ka wannan dalilin ya sa ta samu gagarumar nasara zuwa yau. Dijatu ta samu ilimi sosai domin kasantuwar babbar yayarsu ita ce likita mace ta farko a yankin Arewacin Nijeriya, kuma a suke gida gabanin su ci gaba da karatu, wani yayansu wanda ya dawo daga Rasha kuma ya yi karatun Dokha (Phd) a fanin lissafi, yakan rufesu a gida ya yi ta basu karatu, hakan ya bata zarafi ta samu ilimi daga kowani bangare domin mahaifinsu ma ya taimaka musu wajen fadada ilimi.
Rayuwar Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi aure tun a 1975, Allah Ya albarkace su da da guda daya tilau, kawo yanzu tana da jikoki uku a duniya.