Doddoya
Appearance
Doddoya ganye ne wanda a turanci ake kira Sent leaf/Clove Basil ganye ne mai daɗi da aka sani da ƙamshi da ɗanɗano. Ana noman shi a sassa daban-daban na Najeriya kuma ana daraja shi saboda amfanin magunguna da abinci mai gina jiki. Ganyen kamshi (Ocimum Gratissimum) yana da sunaye iri-iri kamar Nnchanwu (Igbo), Efinrin (Yoruba), da Doddoya (Hausa), Ntong (Efik), da Aramogbo (Edo). Ana yawan amfani da ganyen kamshi wajen shirya nau'ika na miyar Abin I Daba daban kamar Baƙar miyar da miyar Banga. Har ila yau yana ba da rai ga barkono na Najeriya, kamar wannan miya barkono na kaza ko miyar naman akuya.[1]