Dodo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Dodo[gyara sashe | Gyara masomin]

dodo
Dodo
dodo
dodo

Kalmar Dodo a wajen Hausawa dai ta kasu kashi biyu akwai Dodo na sarari da kuma Dodon boye Wanda ake bayyana shi a cikin Tatsuniya a kasar Hausa.

Menene Dodo a kasar Hausa?[gyara sashe | Gyara masomin]

Dodo shi ne abin tsoro ko abin da ido ba ya iya gani ko ya sarrafa shi ko ya yi bayani, kafin zuwan Musulunci kasar Hausa aljanu ne ake bautawa su ne ubangiji.

Kalmar Dodo dai ta kasu kashi biyu akwai Dodo na sarari da Dodon boye wanda ake bayyana shi a cikin Tatsuniyar Hausa a kasar Hausa, a nan sai kaga an siffanta Dodo da aljani abin tsoro wanda yakan iya sarrafa kansa ya cutar da dan Adam, shi kuwa na sarari duk wani abu da idan ido ya gani zai tsorata ko wata inuwa ko fatalwa ko wani abu da ake ba wa yara tsoro da shi, shi a ke kira da wannan kalma.

Kalmar "Dodo" shi ne abin tsoro ko abin da ido ba ya iya gani ko ya sarrafa shi ko ya yi bayani, kafin zuwan Musulunci kasar Hausa aljanu ne ake bautawa su ne Ubangiji.

Me yasa ake jin tsoron Dodo?[gyara sashe | Gyara masomin]

Saboda ana tsoron mutuwa idan an mutu ba za a dawo ba, ana tsoron Dodo saboda zai iya kashe mutum ko ya cutar da shi ko ya sa wa mutum abin da ba zai ji ba dadi, wannan a bangaren babban mutum kenan, shi kuwa a bangaren yaro duk wani abu da za a iya shuna masa ya ba shi tsoro alal misali kunkuniya ko a dauki auduga da zarar an nuna masa sai ya rika jin tsoro wato dai ita wannan kalma ta Dodo duk wani abu da zai bada tsoro wanda kuma ido ba ya iya tabbatar da shi, amma abin da ka sani karara ba a kiransa da sunan Dodo, kamar misali mutuwa tun da an san da za ta zo ta dauki mutum ta tafi, amma duk abin da yake a boye zai iya zuwa ya illata mutum shi ake kira Dod

Ko akwai wani bangare a duniya ne Inda ake fi samun Dodo?[gyara sashe | Gyara masomin]

A ko'ina a ko'ina wani waje ana samun dodo a cikin al'umma suke kuma ko wace alumma akwai nata irin dodon, domun zaka ga misali a kowane yanki zaka ga suna da irin abubuwa kamar kwarangwal da fatalwa da dai dai sauransu. Dan haka kowa da akwai irin abin da suke dauka su yi amfani da shi dan bada tsoro a cikin al'ummar su.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

[1]

  1. https://m.dw.com/ha/shin-mene-ne-dodo-a-wurin-hausawa/a-19143248