Jump to content

Dogecoin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dogecoin
proof-of-work cryptocurrency (en) Fassara, blockchain (en) Fassara, Cryptocurrency da meme coin (en) Fassara
Bayanai
Farawa 8 Disamba 2013
Suna saboda Doge (en) Fassara
Currency symbol description (en) Fassara Ð (en) Fassara
Bisa Litecoin
Inspired by (en) Fassara Doge (en) Fassara
Programmed in (en) Fassara C++ (mul) Fassara
Source code repository URL (en) Fassara https://www.aksmartsupport.com/2023/01/dogecoin-kya-hai-dogecoin-review-in.html
Software version identifier (en) Fassara 1.14.6, 1.10.0, 1.8.3, 1.8.2, 1.8.1, 1.8.0, 1.7.1, 1.7.0, 1.6, 1.5.2, 1.5.1, 1.5.0, 1.4.1, 1.4, 1.3, 1.2, 1.14, 1.14.1, 1.14.2, 1.14.3, 1.14.4 da 1.14.5
Shafin yanar gizo dogecoin.com
Described at URL (en) Fassara coinmarketcap.com…
Lasisin haƙƙin mallaka MIT License (en) Fassara
Copyright status (en) Fassara copyrighted (en) Fassara
Uses (en) Fassara proof-of-work (en) Fassara
Cryptocurrency code (en) Fassara DOGE

Dogecoin, wata irin kuɗin waya da aka ƙirƙira a shekarar Disamba 6, 2013, an fara ta ne a matsayin barkwanci. Duk da haka, yanzu ya zama ɗaya daga cikin manyan kuɗaɗen waya a duniya, musamman godiya ga tallatawa daga fitaccen ɗan kasuwar duniya, Elon Musk Dogecoin yana amfani da tsarin blockchain kamar yadda sauran kuɗaɗen waya ke yi, kuma ana iya amfani da shi don sayayya, bayar da gudummawa, ko kuma a matsayin wata hanyar saka jari.[1]

A tsarin Dogecoin, mining hanya ce da ake amfani da ita wajen tabbatar da ma'amaloli da kuma ƙirƙirar sababbin kuɗaɗe. Masu mining suna amfani da na'urorin kwamfuta masu ƙarfi don warware matsalolin lissafi, wanda hakan ke tabbatar da ma'amala a blockchain. Idan an kammala warware matsalar, ana ba da lada ga mai mining da sabon Dogecoin.[2]

Dogecoin ba shi da iyaka akan adadin tsabar kuɗin da za a iya ƙirƙira, sabanin sauran cryptocurrencies kamar Bitcoin. Kimanin tsabar kudi biliyan 5 ake hakowa a kowace shekara, wanda ke nufin yana da wadatar tsabar kudi da yawa fiye da Bitcoin, inda mafi girman adadin kuɗin da aka taɓa samarwa zai kasance tsabar kuɗi miliyan 21 kawai. Dogecoin yana ɗaukar minti daya kawai don tabbatarwa, yayin da Bitcoin ke ɗaukar mintuna 10.

Elon Musk, wanda shine Shugaban Tesla da SpaceX, ya zama babban mai tallata Dogecoin a yanar gizo. A lokuta da dama, ya yi amfani da Twitter don nuna sha'awarsa game da Dogecoin, har ya kira shi "kudin mutane." Wannan tallafin daga mutum kamar Elon Musk ya taimaka wa Dogecoin wajen samun shahara a duniy.[3]

  1. "Dogecoin spikes more than 20% after Elon Musk says Tesla will accept it as payment for merch". CNBC.
  2. "How To Mine Dogecoin". Forbes.
  3. "Cryptocurrency: Musk's SpaceX to launch dogecoin moon mission". BBC.