Domine Banyankimbona
Appearance
Domine Banyankimbona (an haife ta a shekara ta 1970) [1] tana aiki a matsayin Ministar Sabis na Jama'a, Kwadago da Aiki a Jamhuriyar Burundi. [2] [3] [4]
Tarihi da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Banyankimbona a shekarar 1970 a lardin Bururi. Ita mamba ce ta Cocin Katolika. Banyankimbona ta sami digiri na farko a fannin shari'a daga Jami'ar Hope, Nairobi.[1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Banyankimbona ta taɓa zama mataimakiyar shugaban ɗaya daga cikin kotun kolin ƙasar Burundi sannan ta zama shugabar ƙasa kuma a kotun ɗaukaka kara. Bayan haka, ta zama Shugabar Sashe na Farko na Kotun Shari'a. Banyankimbona ta riƙe muƙamai daban-daban da suka shafi sana'arta kafin ta zama ministar ma'aikatan gwamnati, kwadago da ayyukan yi da shugaban ƙasar Burundi Evariste Ndayyimiyishe ya naɗa.[4][5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Domine BANYANKIMBONA" (in Faransanci). Retrieved 2021-09-24.
- ↑ "Ministère de la Fonction Publique, du Travail et de l'Emploi". www-ministerefptss-gov-bi.translate.goog. Archived from the original on 2021-09-24. Retrieved 2021-09-24.
- ↑ "Une Equipe de Quatre Ministres Inaugure l'Usine Banane de la CAPAD - [Confédération des Associations des Producteurs Agricoles pour le développement]". www-capad-info.translate.goog (in Faransanci). Archived from the original on 2021-09-24. Retrieved 2021-09-24.
- ↑ 4.0 4.1 "Vers la validation de la PANEJ – IWACU". www.iwacu-burundi.org. Retrieved 2021-09-24.
- ↑ "Women occupy 30% of Burundi's new cabinet".