Jump to content

Effiong Okon Eyo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Effiong Okon Eyo
Rayuwa
Haihuwa 1918
Mutuwa 1983
Karatu
Makaranta Kwalejin Gwamnati Umuahia
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Effiong Okon Eyo (1918 - 1983) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki, yankin Gabashin Najeriya. Tun asali Eyo dan jam’iyyar NCNC ne amma bayan takun saka da shugaban jam’iyyar, Azikiwe ya koma jam’iyyar adawa. Bayan haka, ya shiga cikin takardar koke na binciken al’amuran bankin nahiyar Afrika da kuma dangantakar bankin da gwamnatin yankin a shekarar 1956.[1]

  1. Sklar, Robert (2015). FacebookTwitterEmailMore Nigerian Political Parties Power in an Emergent African Nation. Princeton University Press. p. 161. ISBN 9781400878239.