Jump to content

Elsie Uwamahoro

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Elsie Uwamahoro
Rayuwa
Haihuwa 23 Oktoba 1988 (36 shekaru)
ƙasa Burundi
Sana'a
Sana'a swimmer (en) Fassara

Elsie Uwamahoro (an haife ta a ranar 23 ga watan Oktoba, 1988) 'yar wasan ninkaya ce 'yar ƙasar Burundi. Ta shiga gasar Olympics ta lokacin zafi a shekarar 2008 da aka yi a birnin Beijing, da kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin rani ta shekarar 2012 da aka yi a birnin Landan, kuma tana matsayi na 67, wanda bai kai Uwamahoro zuwa wasan kusa da na karshe ba. [1] Ta kuma yi gasar tseren mita 50 da 100 a gasar tseren ruwa ta duniya ta shekarar 2013.

A shekarar 2016, ta shiga gasar tseren mita 50 na mata a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2016 da aka gudanar a Rio de Janeiro, Brazil. Ta kare a matsayi na 80 a cikin heat da maki 33.70 kuma ba ta tsallake zuwa matakin kusa da na ƙarshe ba. [2]

  1. Evans, Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill; et al. "Elsie Uwamahoro". Olympics at Sports-Reference.com. Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 3 August 2012.
  2. "Swimming Results Book". 2016 Summer Olympics. Retrieved 28 July 2020.