Faifan DVD PLAYER
Faifan DVD PLAYER | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | consumer electronics (en) da dvd & blu-ray player (en) |
Uses (en) | DVD (en) |
Na’urar DVD Player wacce aka samar tare da fasahar DVD ta biyo bayan fasahar CD wadda sanadiyyar naqasun da suka bayyana na rashin juriya, da rashin qarko da kuma qarancin mizanin ma’adana,Sai aka samu canji da fasahar DVD. Samar da faifan DVD ya haifar da samuwar na’urar sarrafa faifan DVD, kamar yadda samar da faifan garmaho ya haifar da samuwar na’urar sarrafan faifan garmaho (Gramophone Player), a lokuta ko zamanin baya.[1]
Na’urar sarrafawa da bayyana bayanan dake sauke cikin faifan DVD ita ake kira da DVD Player. Wannan sarrafa faifan CD, saboda bambancin nau’in bayanan da faya-fayan ke sauke dasu, da kuma bambancin asalin fasahohin da aka yi amfani dasu wajen samar da su.
Amfani
[gyara sashe | gyara masomin]Na’urar DVD Player na amfani da nau’in hasken lantarki na leza ne, wato Laser Light, launin ja, wajen karva, da sarrafawa da kuma bayyana bayanan da ake zuba mata a farkon lamari ko a duk sadda aka tashi sabunta su, idan faifan nau’in Re-Writable ne, wato: DVD-WR. Wannan tsari ya dara na CD nesa ba kusa ba. Sannan yana sauke ne da fasahar dake iya tsallakawa daga fallen farko zuwa falle na biyu, idan faifan mai tagwayen falle ne, wato: “Double Layer DVD”.
Nau`i
[gyara sashe | gyara masomin]Na’urar sarrafa DVD na zuwa nau’i-nau’i ne. Akwai nau’in gama-gari, wato na’ura ta musamman mai zaman kanta, wacce aka qera don sarrafawa da kuma kallo ko mu’amala da bayanan dake xauke cikin faifan DVD. Wannan ita ce aka fara qerawa a farkon bayyanar faifan DVD.[2]