Fanken Fulawa
Fanke Fulawa wani abinci ne na hausawa wanda suke cin shi da shayi ko kunu ko kuma kayan sanyi irinsu zobo da sauran su fanke yana da dadi sosae ga amfani a jikin dan adam, ana hada shine da fulawa a soya shi a cikin ruwan mai mai zafi. kuma yana da laushi sosae. [1]
Kayan Hadi
[gyara sashe | gyara masomin]Abubuwan da za a bukata
• Bota
• Kwai
• Madarar fulawa • Fulawa • Sukari
• Bakar hoda/ Yeast
• Gishiri kadan
• Filebo[2]
Yadda ake Hadawa
[gyara sashe | gyara masomin]Hadi
A samu fulawa a tankade ta sannan a jika sukari a dama da ruwa kadan a kofi a yi ta gaurayawa har sai ya narke. A zuba fulawa a kwano, a zuba bota kamar cokali 2, a dirza ta da fulawa har sai ta bata a cikin fulawa. Sannan a zuba yeast kamar cokalin shan shayi biyu a ruwan dumi a jira na kamar minti 5, bayan minti 5 za a ga ya dan yi kumfa a saman kofin. Sannan a zuba madarar fulawa da gishiri rubu’in cokalin shan shayi da filebo, a fasa kwai kamar biyu. Sannan a ci gaba da murzawa. A zuba ruwan yeast a kwaba sannan, a dauko ruwan sukarin nan a zuba ana kwabawa har sai yadan yi kauri haka daidai kwabin fanke. Bayan sun kwabu sosai. Sai a rufe na tsawon yini guda. Wadansu kuma za su iya jiransa sai ya tashi kafin tuya. [3] Bayan kwabin ya tashi, sai a dora man gyada a tukunyar tuya a yanka albasa. Bayan ya yi zafi sai a rika yankawa daidai girman fanken da ake so. Har sai sun toyu sannan a kwashe a sanya wa maigida a kwanon karyawarsa.
Za a iya cin wannan fanken da shayi ko kunu kuma ya fi dacewa da karyawa. [4] [5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-02-01. Retrieved 2023-03-15.
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/yadda-ake-yin-fanke/
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/yadda-ake-yin-fanke/
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/yadda-ake-yin-fanke/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-02-01. Retrieved 2023-03-15.