Fatima Ali Modu Sheriff
Fatima Ali Modu Sheriff (an haife ta a shekarar 1964), a birnin Maiduguri, Jihar Borno Najeriya.[1]
Kuruciya da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Fatima a shekara ta alif 1964 a gabashin Najeriya Maiduguri, jihar Borno. Ta fara karatun ta na firamare a makarantar Shehu Gabai Primary School, Maiduguri. A tsakanin shekarun alif 1970 zuwa 1980s ta zama daliba a Polytechnic na Maiduguri inda ta yi karatu akan gudanar da kasuwanci (Business management).
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Fatima Modu tana da matukar tausayi musamman ga mata da kananan yara. Hakan yasa tayi fice ta fuskar tallafin kudi da magunguna ga yara da mata. Ta rike mukamai da dama na ma’aikatu masu zaman kansu. Tana daga cikin kusoshin kungiyoyin mata kamar National Council for Women Societies, Nigerian Association of Women Journalists among others.
Nassi
[gyara sashe | gyara masomin]Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.