Jump to content

Fatima zarah umar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Fatima zarah Umar

Fatima Zarah Umar ta kasance babbar mai fafutukar kare hakkin mata ce, ta kasance lauya, 'yar jarida kuma 'yar siyasa. Ita ce tsohuwar mai masaukin baki a shirin Adikon zamani na BBC wanda ya kalubalanci imani da ayyuka masu cutarwa. A halin yanzu tana aiki a Majalisar Dokoki ta kasa a matsayin mataimakiya ta musamman kan jinsi ga shugaban majalisar dattawa. Ita kuma ƙwararriyar karatun littafi ce kuma tana son yin tafiye- tafiye.