Fauziah Mohd Taib
Fauziah binti Mohamad Taib (an haife shi a ranar 26 ga watan Maris na shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da Bihar(1965)) jami'in diflomasiyyar Malaysia ne kuma marubuci. Ta kasance a baya Jakada a Masarautar Netherlands, mukamin da ta rike daga ranar 13 ga watan Agusta shekarata 2008 har zuwa lokacin da ta yi ritaya a shekarar 2015. [1]
Ayyukanta na farko da aka buga, mai taken Malaysia da UNCED: An Analysis of A Diplomatic Process, an buga shi a ƙarƙashin Kluwer Law International a cikin shekarata alif 1989 kuma ya kasance mai magana game da tsarin tattaunawar diflomasiyya. Littafinta na baya-bayan nan, A the OPCW: A Story of Malaysia's Interventions, Darakta Janar ne ya ƙaddamar dashi a watan Maris na shekara ta 2015.
A shekarata 2005, an nada Fauziah a matsayin Darakta Janar na Cibiyar diflomasiyya da alakar kasashen waje, ƙungiyar horo ta Ma'aikatar Harkokin Waje (Malaysia) .
Ministan Harkokin Waje yayi amfani da ƙwarewarta ta rubuce-rubuce a wannan lokacin a matsayin jagoran marubucin jawabinsa. An santa da ƙarfinta a cikin batutuwa masu mahimmanci da kuma ƙwarewar rubutu.
Lokacin da aka ba OPCW kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekarar 2013, babu wata tambaya cewa Fauziah zai kasance daga cikin 'yan wakilan jihar dake tafiya zuwa Oslo don bikin. [2]A cikin Netherlands, Fauziah ta gano baiwa don zanen kuma ta gudanar da nune-nunen ta na farko a The Hague a shekarar 2012.
Fauziah mai sha'awar tafiya ce - sha'awar da ta ci gaba bayan ta kwashe lokacin rani na kammala karatunta a shekarar alif 1977 tana tafiya da tafiya a fadin nahiyar Amurka.
- ↑ "Official Website of Embassy of Malaysia, The Hague". Archived from the original on 12 August 2014. Retrieved 11 August 2014.
- ↑ "Malaysian is part of Nobel Peace Prize winning team".