Jump to content

Fidèle Moungar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fidèle Moungar
Prime Minister of Chad (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Doba (en) Fassara, 1948 (75/76 shekaru)
ƙasa Cadi
Karatu
Harsuna Larabci
Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Fidèle Abdelkérim Moungar (an haife shi a shekarar 1948) ɗan siyasan ƙasar Chadi ne wanda ya yi aiki a matsayin Firayim Minista na Chadi a 1993. A yanzu haka shi ne Sakatare-Janar na Chadian Action for Unity and Socialism (ACTUS), wadda ta kasance jam'iyyar adawa ta hagu.

Moungar dan asalin ƙabilar Sara ne, an haife shi a shekarar 1948 a Doba a cikin Logone Oriental Region. Ya yi karatun aikin likita na tiyata a Faransa. Ya fara siyasarsa lokacin da aka samu wasu 'yan waren jam'iyya inda ya kafa ACTUS, jam'iyyar da ke adawa da FROLINAT da kuma wadel Abdelkader Kamougué wadda a zahiri ke riƙe da gwamnatin kudancin Chadi, Comité Permanente du Sud, a cikin Mayun shekarar 1979 a Paris .

An haifi babbar 'yar Moungar Vanessa Moungar a shekarar 1984 kuma tana aiki a Bankin Raya Kasashen Afirka.

 

Political offices
Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}