Filin jirgin sama
filin jirgin sama | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | aerodrome (en) , station (en) da ma'aikata |
Has characteristic (en) | airport security (en) |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Filin jirgin sama wuri ne na musamman da aka samar masa da na'urori na zamani da ma'aikata domin sauka tare da tashin jiragen sama.
Filin jirigin sama ya ƙunshi abubawa da dama waɗanda ake buƙata na musamman domin samar da cikakkun tsaro, kulawa, walwala, samar da cikakkun na'urorin zamani da samar da bayanai waɗanda suka shafi kula da tashi da kuma saukan jiragen saman. Yana kuma ɗaya daga cikin abubuwan da aka samar wa filin jirgin, sune:- dogon titi wanda zai wadaci jirgi yayi gudun mai nisa, wanda zai taimaka masa wurin tashi sama da kuma sauka ƙasa, wadataccen filin ajiye jiragen sama.
Manyan filayen jiragen musamman na ƙasa da ƙasa, sunada wurare na musamman inda jami'an kwastom da na immigration ke kula da shige da ficen matafiya. Haka kuma ana samun gidajen sayar da abinci, bankuna da kuma manyan kantuna na zamani duk a cikin su.