Filin jirgin sama

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wikidata.svgfilin jirgin sama
Heathrow Airport 010.jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na aerodrome (en) Fassara da station (en) Fassara
Has quality (en) Fassara airport security (en) Fassara
Filin jirgin saman Zürich, Switzerland
Filin jirgin saman Tampere, Finland

Filin jirgin sama wuri ne na musamman da aka samar masa da na'urori na zamani da ma'aikata domin sauka tare da tashin jiragen sama.

Filin jirigin sama ya ƙunshi abubawa da dama waɗanda ake buƙata na musamman domin samar da cikakkun tsaro, kulawa, walwala, samar da cikakkun na'urorin zamani da samar da bayanai waɗanda suka shafi kula da tashi da kuma saukan jiragen saman. Yana ɗaya daga cikin abubuwan da aka samar wa filin jirgin, sune:- dogon titi wanda zai wadaci jirgi yayi gudun mai nisa, wanda zai taimaka masa wurin tashi sama da kuma sauka ƙasa, wadataccen filin ajiye jiragen sama.

Manyan filayen jiragen musamman na ƙasa da ƙasa, sunada wurare na musamman inda jami'an kwastom da na immigration ke kula da shige da ficen matafiya. Haka kuma ana samun gidajen sayar da abinci, bankuna da kuma manyan kantuna na zamani duk a cikin su.

Manazart[gyara sashe | gyara masomin]