Filin jirgin saman Cotonou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Filin jirgin saman Cotonou filin jirgin sama ne a cikin unguwar Cadjehoun na Cotonou, birni mafi girma a cikin Benin, a Yammacin Afirka. Filin jirgin saman shine mafi girma a cikin ƙasar, kuma saboda haka, shine farkon hanyar shiga ƙasar ta jirgin sama, tare da tashi zuwa Afirka da Turai.

Sunan filin jirgin ya samo asali ne daga Cardinal Bernardin Gantin

Hadari da abubuwan da suka faru[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Jirgin UTA 141 A ranar 25 ga watan Disamban shekara ta 2003, jirgin ya fado a Bight of Benin, ya kashe 151 daga cikin 163 da ke ciki, yawancinsu 'yan Kasar Lebanon.

A cikin shekara ta 1974, an yanke shawarar matsar da ayyukan filin jirgin saman Cotonou zuwa wani sabon wuri a cikin Glo-Djigbé . Rashin kuɗaɗe ya dakatar da aikin cikin sauri.

A halin yanzu, an fara inganta filin jirgin saman Cotonou.