Jump to content

Garin Kakihum

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kakihum Kauye ne dake karamar hukumar mariga, a jihar neja, najeriya.

Garin kakihum garine daya samo asali tareda mazauna masu yawa tun kakanni da kakanni. Garin na girkene a tsakiyar tsaunuka hudu, wadanda suka hada da Dutsen mailamba, a gabashin garin, dutsen yamma, a yammacin gari, da kuma duwatsun kudu da arewa. Garin ya samo asaline daga kabilun kambari, acifawa, da hausawa. Wanda kuma hausawa sune suka gaje garin a yanzu. Harwayau akwai kambari da dama wadanda kambarin sun hada da kambarin Kishina. Akwai bangarorin cigaba, musamman bangaren ilimi, noma dakuma kasuwanci. Masarautar kakihum na daya daga cikin masarautun da sukayi yaki a lokacin sarki Nagwamatse dake kontagora. Sarki Sale shine sarki na farko a masarautar kakihum.

Garin Kakihum yana ayankin da ya haɗa magama da kumbashi, maburya, bangi da kuma shadadi, duk a jihar neja din.

1.Yahuza Sa'idu BKY Kakihum dalibi a kwalejin koyon aikin karantarwa dake garin kontagora dake jihar neja.