Jump to content

Gautam Chakroborty

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Gautam Chakroborty (1954 - 27 ga watan Mayu shekarar dubu biyu da ashirin da biyu 2022) dan siyasan Jam'iyyar Nationalan Bangladesh ne kuma memba Jatiya Sangsad mai wakiltar mazabar Tangail-6. Ya kuma kasance karamin ministan albarkatun ruwa.

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Gabashin Pakistan, Gautam ya sami ilimi har zuwa LLB.

An zabi Chakroborty a matsayin dan majalisa daga Tangail-6 (Nagarpur-Delduar) a 1996 da 2001 a matsayin dan takarar jam'iyyar Nationalist ta Bangladesh (BNP) ya doke dan takarar Bangladesh Awami League Khondokar Abdul Baten sau biyu. Ya samu takarar ne daga jam’iyyar a babban zaben Bangladesh na 2008 amma ya sha kaye a hannun Ahasanul Islam Titu na Awami League. [1]

Chakroborty ya mutu daga bugun zuciya da rana/ maraice bisa ga rahotanni a ranar 27 ga Mayu 2022. [2]

  1. "Get 11th Bangladesh National Election 2018 Results". The Daily Star (in Turanci). 14 November 2018. Retrieved 23 September 2020.
  2. "Former state minister Gautam Chakraborty dies". Dhaka Tribune. 27 May 2022. Retrieved 27 May 2022.