Gulma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Gulma ita dai gulma ko kuma muce giba duk suna nufin abu ɗaya wato yi da mutum ko kuma sukar mutum a yayin da baya kusa ko kuma kai sukar mutum gurin wani na gaba dashi. Gulma hanya ce ta tozarta mutane wadda duk mai yinta ƙarara yake shi ba mutumin kirki bane don zai iya yin gulmar kowa musamman ace ya maida ta sana'ar sa. Sannan gulma tana ragewa mai yinta daraja da girma a gurin mutane musamman idan aka fahimci mutum shi magulmaci ne. Kuma gulma tana haɗa faɗa. A addinin Musulunci gulma babban zunubi ne wanda har sai mutum ya nema yafiyar wanda yaci namanshi, sannan kuma ya nemi yafiyar Allah Subhanahu wata'ala.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]