Haƙƙin faɗar magana
Appearance
Haƙƙin faɗar magana | |
---|---|
exception to copyright (en) | |
Bayanai | |
Has characteristic (en) | quotation (en) |
Haƙƙin faɗi ko haƙƙin zance ko haƙƙin magana yana ɗaya daga cikin haƙƙin mallaka (copyright) da Yarjejeniyar Berne ta bayar a cikin maƙala ta 10: “ An halatta a faɗa magana"... matuƙar fadar ta ya dace da aiki na gaskiya, kuma iyakarsu ba ta wuce abin da aka tabbatar da manufar ba”. [1]Tare da harsuna daban-daban, duk da an riga ta kasance a cikin sake fasalin 1908 na yarjejeniyar. [2]
Aiwatarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Dokokin ƙasa yawanci suna ɗaukar iyakokin al'ada (Berne Convention) a ɗaya ko fiye daga cikin abubuwan da ake buƙata masu zuwa:
- Sunsyen da aka kawo suna cikin iyaka mai ma'ana da kuma (banbanci daga wannan ƙasa zuwa waccan ƙasar),
- Wadda a fili yake an bayyana alamar cewa magana ce da take da cikakken bayani.
- Sakamakon sabon aikin ba kawai tarin yin magana ba ne, amma ya ƙunshi cikakken aikin asali a cikin kansa.
A wasu ƙasashen maƙasudin yin amfani da aikin (ilimi, kimiyya, ɓarna da sauransu) na iya zama wani abu da ke ƙayyade iyakar wannan haƙƙin na yin magana ko faɗa.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Convention for the Protection of Literary and Artistic Works
- ↑ «As regards the liberty of extracting portions from literary or artistic works [...] is not affected by the present Convention.» Convention for the Protection of Literary and Artistic Works (Berlin Act, 1908).