Hae Hae Te Moana River
Kogin Hae Hae Te Moana kogi ne dake cikin yankin Canterbury wanda yake yankin New Zealand. Yafara samo asali ne a cikin Kololuwa hudu na arewa wanda yake reshan Kudancin Alps, tare da Reshen Arewa da Reshen Kudu wanda ke haɗuwa zuwa arewacin Pleasant Valley . Kogin yana gudana kudu maso gabas don shiga kogin Waihi kusa da Winchester . Kogin da aka hade ana kiransa Kogin Temuka, wanda ya ratsa Temuka don shiga kogin Opihi jim kadan kafin ya shiga cikin Canterbury Bight .
Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]
- Jerin koguna na New Zealand