Hairatu Gwadabe
Hairatu Gwadabe |
---|
Hairatu Gwadabe (An kuma haife ta a shekara alif ɗari tara da hamsin da takwas 1958A.c), daga zuri’ar Ashafa.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Tayi makarantar Capital School Kaduna, daga nan ta tafi Government Girls College, Dala Kano. sannan Tayi Diploma a Shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello. Tayi digirinta a fannin shari’a a shekarar 1976.[1]
Rayuwa Aure
[gyara sashe | gyara masomin]Ta kuma auri Colonel Lawan, suna da yara guda biyar (5) wanda a cikin su daya ta mutu tare da ita.
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]A addinin musulunci mutuwar shahada yana daga cikin mutuwa masu daraja, inda duk wanda yayi dace da shahada to aljanna zai tafi kai tsaye. Daga cikin mutuwan shahada a musulunci. Akwai wanda ruwa ya ci shi. Wanda ciwon ciki ya kashe shi. Wanda gini ya fado mashi. Wanda ya kone har ya mutu. Wanda ya mutu wajen yakin musulunci. Hairatu ta mutu da yarta guda daya cikin wuta, inda wuta ya kona su, har suka mutu.[1]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN 978-978-956-924-3. OCLC 993295033.