Haji Wright
Appearance
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Haji Amir Wright (an Haife shi ga watan Maris 27, 1998) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Amurka wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ko wiwi don ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta EFL Championship Coventry City da ƙungiyar ƙasa ta Amurka.
Bayan ya fara taka leda a New York Cosmos a shekara ta 2015, ya shafe mafi yawan aikinsa a yankin nahiyar Turai, tare da Schalke 04 a Bundesliga na Jamus, VVV-Venlo a Dutch Eredivisie, SønderjyskE a Danish Superliga da Antalyaspor a Turkiyya Süper Lig.
Wright ya fara taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Amurka a shekarar 2022 kuma ya taka leda a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022.[1]