Jump to content

Hajiya Haidzatu Ahmed

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hajiya Haidzatu Ahmed
Rayuwa
Haihuwa 1966
ƙasa Najeriya
Mutuwa 25 ga Yuni, 2021
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Hajiya Haidzatu Ahmed wata basarautar gargajiya ce ta Najeriya wacce ta yi sarauta a matsayin Sarauniyar Kumbwada tun 1998. A matsayinta na sarauniya, ta yi fatali da fatattakar cin zarafin mata a cikin gida kuma ta kasance mai goyon bayan ilimin mata.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Hajiya ita ce mai mulki a tsohuwar masarautar Kumbwada a kasar Nijar, mai yawan jama'a kusan 33,000.[1][2]. Ta gaji kakarta a matsayin sarauniyar masarauta wadda mata ke mulki a shekarar 1998.[3][4][5] ‘Yarta Idris ita ce magaji.[1] Tana kuma da da, Danjuma Salih.[6]

A matsayinta na sarauniya, Hajiya tana warware rikicin aure da filaye, tana kiyaye zaman lafiya, kuma mai ba da shawara ce ga ilimin mata.[1] A 2010, ta shaida wa CNN cewa, "Dole ne mata su kasance masu ilimi, ilimi yana nufin mata za su iya zama duk abinda suke so"[1] Ta yi hukunci mai tsauri kan kisan aure da cin zarafin mata a Kumbawada, sarauniya ta ba wa mata damar sauraren karar[

Ita musulma ce.[2]

  1. 1.0 1.1 "Hajia Ahmed: Nigeria's only queen in a land of kings - CNN.com". www.cnn.com.
  2. "Life-Sized Portraits of the Kings and Queens of Nigeria".