Harin bam a Maiduguri, Janairu 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harin bam a Maiduguri, Janairu 2014

Da misalin karfe 1:30 na rana ranar 14 ga watan Janairun 2014, wata mota makare da bama-bamai ta tashi a birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya. [1] [2] Bam din wanda ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 17, ya fashe ne a gaban ofisoshin gidan talabijin na ƙasar da ke kusa da wata kasuwa. [1] [2] Rundunar soji ta ce an kama wani da ake zargi. [2] Ƙungiyar Boko Haram mai da’awar jihadi - wacce ta kai hari Maiduguri fiye da kowane birni [3] - ta ce ita ce ta kai harin. [2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]