Hawainiya
Hawainiya | |
---|---|
Scientific classification | |
Kingdom | Animalia |
Phylum | Chordata |
Class | Reptilia (en) |
Order | Squamata (en) |
dangi | Chamaeleonidae Rafinesque, 1815
|
Geographic distribution | |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Hawainiya na ɗaya ce daga cikin halittun dabbobi da Allah ya halitta a doron ƙasa, Kuma babu shakka akwai abin al'ajabi game da yadda hawainiya take haihuwar ƴaƴanta, da kuma hanyar da ƴaƴan ta suke zuwa duniya. Kuma ko shakka babu akwai darasi da dan Adam ya kamata ya ɗauka daga tsarin haihuwar hawainiya.
Da farko dai, idan hawainiya ta ɗauki ciki, to namijin ne zai je ya haƙa rami, ita kuma matar sai ta zo namijin ya binne ta a ramin da ranta. Wani lokaci takan shiga salin alin, wani lokaci kuma sai sun yi kokuwa da namijin ya galabaitar da ita, sannan ya tura ta cikin ramin ya binne ta. A haka za ta mutu ta ruɓe, ƴaƴan cikin nata su ƙyanƙyashe sannan su fito duniya. Kuma ko da ruwan gatari ko wani ƙarfe mai faɗi aka sa a kan kabarin nata, idan dai lokacin fitowar ƴaƴan ya yi, haka za su huda wannan ruwan gatarin ko ƙarfen su fito. Kuma tun da Allah ya halicci hawainiya haka take haihuwa bata taɓa fasawa ba.
Darasin da ke tattare da tsarin haihuwar hawainiya shi ne cewa, babu wata hawainiya da ta taɓa morar ɗanta a duniya, tun da sai ta mutu sanan ƴaƴanta suke zuwa duniya. To ina ga ɗan Adam, kai da Allah ya ƙaddara zaka haifi ƴaƴanka, su girma, har ka riƙa alfahari da su, amma sai mutum ya riƙa watsi da ƴaƴansa, bai ma damu da rayuwarsu ba. Yau da ace ta hanyar da hawainiya take haihuwa, haka ma ɗan Adam yake haihuwa, ina mutum zai kai ƙara? Babu.
Don haka ya kamata mutane su godewa Allah, wanda ya ƙaddara musu haihuwa bisa tafarkin da za su mori ƴaƴansu domin su amfani kansu da iyayensu da ma al'ummar da suke rayuwa a cikinta. Kuma ya zama wajibi ga iyaye su ɗauri aniyar kuɓutar da ƴaƴansu daga bala'o'i da masifu na rayuwar Yau DA kullum
Ta yaya Hawainiya take haihuwa