Jump to content

Hawan Daushe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hawan Daushe ya kasance al'adar hawa ne da sarki kanyi a yayin bikin sallah karama ko Babba, inda mahaya dawaki tare da yan gari kanci kwalliya da ado don su tarbi sarki.[1]

Manazarta

Yadda aka yi hawan Daushe a Kano

12 Aprilu 2024

Mai marataba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi hawan Daushe da yammacin ranar Alhamis tare da hakimansa. Hawan Daushe zagaye ne da mai martaba Sarkin Kano ke yi tare da hakimansa nasa a kan dawakai cikin ado da farin ciki, inda mutanen gari kuma ke kai gaisuwa da caffa. Tawagar na farawa ne daga kofar arewa ko kuma kofar kwaru zuwa kofar kudu na masarautar ta Kano, inda ake sukuwa a gaban manyan baki daga gida da wajen Najeriya, kafin daga bisani Sarki ya yi ban bankwana ya shiga gida.

Jerin haye-hayen da ake yi a Kano:

  • Hawan Sallah
  • Hawan Daushe
  • Hawan Nassarawa
  • hawan fanisau
  • Hawan Dorayi
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-05-13. Retrieved 2023-05-13.