Jump to content

Hayatu ibn Sa'id

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Shehu Hayatu Ibn Sa'id (1840-1898), wanda kuma aka sani da Hayatu Balda, babban malamin musulunci ne na ƙarni na 19, kuma jagoran mahadiyya a yankin tsakiyar Sudan.Shine jikan Usman Dan Fodio wanda ya jagoranci jihad na Sokoto kuma sarkin farko na Sokoto.Hayatu ya bar Sokoto a ƙarshen shekarun 1870s ya koma garin Adamawa, emirate da ke karkashin gabashin wannan mulkin.A shekarar 1883 an nada shi matsayin mataimakin Mahdi na Sudan ,Muhammad Ahmad,kuma an bashi aikin jagorantar jihad akan Daular Sokoto.Duk da wasu kokarin da Lamido Zubeiru na Adamawa yayi na shawartar Hayatu ya daina goyon bayan mahadiyya, ya haifar da rikici wanda ya haifar da faduwa mai ban tausayi ga sojojin Zubeiru a cikin 1893.Wannan nasara ta karfafa mabiya da kuma tasirin Hayatu,wanda ya haifar da haɗin gwiwa da Rabih az-zubayr,wani babban dan fama daga sudan wanda ke goyon bayan mahadiyya. Tare sunyi nasarar mamaye gidan mulkin Bornu da ya zamo mai rauni a cikin 1893, suna nufin daga karshen su mamaye daular Sokoto.Hayatu ya kasance imamin Bornu ta Rabih, yana aiki a matsayin jagoran ruhaniyya.Duk da haka, haɗin gwiwar ya karye a karshe,kuma Hayatu ya mutu yayin kokarin tserewa daga Bornu a cikin 1898.