Jump to content

Herbert Wigwe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hoton Herbert Wigwe

Herbert Wigwe, (an haifeshi ranar 15 ga Agusta, 1966), wanda iyayensa yan jihar Ribas ne. Yana da 'yan'uwa mata uku masu suna kamar Joyce, Peggy, da Stella da ɗan'uwa ɗaya Emeka.[1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Ya halarci Kwalejin St. Gregory da ke Legas inda ya yi karatun sakandire sannan ya wuce Jami’ar Najeriya da ke Nsukka, inda ya samu digiri a fannin lissafi watau da turanci ake kira da accounting a shekarar 1987.[1] Ya ci gaba da karatunsa ta hanyar samun digiri na biyu a fannin Banki da Kudi watau banking and finance daga Jami'ar College of North Wales (yanzu Jami'ar Bangor) a 1989 da kuma wani digiri na biyu a fannin tattalin arziki daga Jami'ar London a 1990.[1] Ya kuma halarci Makarantar Kasuwanci ta Harvard don kari karatu akan ilimin gudanarwa a 2006.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]