Hukumar Bunƙasa Ci Gaba, Canjin Tsari da Aiki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hukumar Ci gaba, Canjin Tsarin da Aiki;(Jamus: Kommission für Wachstum, Strukturwandel und Beschäftigung</link>(WSB), asali Kommission für Wachstum, Strukturwandel und Regionalentwicklung</link>, wanda aka fi sani da Kohlekommission, wato hukumar kwal, a Jamus) kwamiti ne da gwamnatin tarayyar Jamus ta ƙirƙira akan 6. Yuni 2018, bayan haɗin gwiwar jam'iyyar Christian Democrats (

CU/ CSU) tae da Social Democrats (SPD)a cikin Fabrairu 2018.

Ya kamata kwamitin ya mika rahotonsa na ƙarshe ga gwamnatin tarayya a ranar 1 ga Fabrairu 2019. Ana sa ran ƙaddamar da matakan da aka ba da shawarar game da ci gaban zamantakewa da tsari da kuma ba da kuɗaɗen Jihohi, waɗanda ake hako gawayin launin ruwan kasa, a ƙarshen Oktoba 2018. Ya kamata Waɗannan matakan sun haɗada matakan dakile sauyin yanayi, musamman shirin kawar da gurbataccen mai tare da ranar karewa da matakan cimma burin rage fitar da iskar gas nan da shekarar 2020 da Jamus ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.

An buga rahoton hukumar a watan Janairun shekarar 2019 yana bada shawarar Jamus ta kawar da baki ɗaya tare da rufe sauran 84 da suka rage masu aikin kwal a yankinta nan da 2038. Yayin da wasu suka yaba da wannan a matsayin nasara, wasu, ciki harda masana kimiyya da masana yanayi, sunyi iƙirarin cewa har yanzu wannan ba zaiyi sauri sosai ba, kuma don hana yanayin daga kaiwa ga wani matakin da ba za a iya jurewa ba, tilas ne a kawar da shi nan da shekara ta 2030.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]