Immaculée Nahayo
Immaculée Nahayo | |||
---|---|---|---|
2005 - 2007 ← Jean Minani (en) - Pie Ntavyohanyuma (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Commune of Gatara (en) , 1948 | ||
ƙasa | Burundi | ||
Mutuwa | City of Brussels (en) , 17 Nuwamba, 2018 | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | National Council for the Defense of Democracy–Forces for the Defense of Democracy (en) |
Immaculée Nahayo Nyandwi (1948 - 17 Nuwamba 2018) 'yar siyasa ce 'yar Burundi wacce ta kasance Shugabar Majalisar Dokokin Burundi daga ranar 16 ga watan Agusta 2005 zuwa 2007, [1] mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a Burundi. An kuma zaɓe ta a matsayin shugabar kungiyar 'yan majalisu ta Afirka (APU) zuwa watan Maris 2007.
Aikin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]'Yar ƙabilar Hutu ce ta majalisar National Council for Defence of Democracy-Forces for Defence of Democracy (CNDD-FDD), ta maye gurbin Jean Minani na Front for Democracy a Burundi (FRODEBU), wanda ya kasance shugaban majalisar dokokin ƙasar tun a 2002.
Daga baya ta yi aiki a matsayin ministar haɗin kai ta ƙasa, komowa, sake gina ƙasa, kare hakkin ɗan Adam, da Jinsi tun daga watan Yuli 2007.[2] An zaɓe ta a matsayin mai ba da shawara a COMESA.
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]An haife ta a Gatara (Lardin Kayanza), Nahayo ta kasance mahaifiyar ’ya’ya shida. Mijinta, Simon Nyandwi, ya kasance ministan cikin gida har zuwa mutuwarsa a ranar 22 ga watan Maris 2005.
Nyandwi ta mutu a ranar 17 ga watan Nuwamba 2018 a Brussels, Belgium, tana da shekaru 70. [3]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jerin sunayen shugabannin majalisar dokokin Burundi
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "HISTORIQUE - Assemblée Nationale du Burundi". www.assemblee.bi. Archived from the original on 2023-09-30. Retrieved 2024-03-25.
- ↑ Burundi - World Leaders Archived 2011-08-13 at the Wayback Machine: Chiefs of State and Cabinet Members of Foreign Governments. Central Intelligence Agency, Date of Information: 4/1/2011. Retrieved 2011-08-14.
- ↑ "Burundi : Décès de l'Hon Nahayo Immaculé, épouse de Feu Nyandwi Simon – nouvelles du Burundi Africa Generation News" (in Turanci). Retrieved 2019-02-08.