Insha’i
Insha’i wani gajeren rubutu ne wanda ka iya zamowa labari, bayani, wasika ko kuma muhawara. Abin da aka rubuta kuma yana iya zamowa tabbatacce ne wanda ya taba faruwa ko kuma kirkirarre. Babban amfanin insha’i shi ne, koyawa yara ‘yan makaranta dabarun yin rubututtuka.
Menene insha'i: insha'i shine rubuta labari ko jawabi mai ma'ana tare da bin ka'idodin rubutu.
Rukunan Insha’i
[gyara sashe | gyara masomin]Abin da ake nufi da Rukuni a nan shi ne (sashe). Zamowar insha’i gajeren rubutu bai hana shi samun sassa ba domin ya samu cika. Insha’i yana da rukunai guda uku kamar haka:
- Gabatarwa.
- Gundari jawabi.
- Kammalawa.
Abun so ne insha’i ya samu wadannan sassa guda uku, rashin samun daya daga cikin su ya mai she da wannan insha’i nakasasshe.
Gabatarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Rukuni ko sashen farko na insha’i shi ne gabatarwa. A wannan sashe na gabatarwa mai rubuta insha’i yake yin dan takaitaccen bayanin da ya ke kunshe da jawabi game da abin da mai rubutun zai yi rubutu a kansa. Ba a son gabatarwa ta wuce sakin layi daya, kuma cikin takaitattaun layuka.
Wannan sashe na gabatarwa, sashe ne mai matukar muhimmanci a fagen rubutun yare. Daga gabatarwa mai karatu yana iya kwadaituwa da karanta wannan rubutu ko kuma rubutun ya gundure shi ya yi watsi da shi baki daya. Saboda haka abu ne mai kyau, mai rubutu ya tsaya ya rubuta kyakkyawar gabatarwa kuma takaitacciya game da abin da yake yin rubutun a kansa.
Gundarin Jawabi
[gyara sashe | gyara masomin]Gundarin jawabi shi ne cikakken rubutun da zai bayyanawa mai karatu asalin abin da ake yin rubutun a kansa. A wannan sashe ne mai rubuta insha’i ya ke daukar abin da ya ke yin rubutu a kansa ya yi bayaninsa dalla-dalla, sannan kuma daki-daki a cikin sakin layi daban-daban.
Kammalawa
[gyara sashe | gyara masomin]Takaitawa ce ta dukkan abin da aka rubuta tun daga gabatarwa har zuwa sakin layi na karshe na cikin gundarin jawabi. Abun so ne kammalawa ta kasance a cikin sakin layi guda, sannan kuma na karshe wanda daga shi ba wani, kuma mai cin gashin kanta.
Abubuwan Lura Wajen Rubuta Insha’i
[gyara sashe | gyara masomin]Dan rubuta nagartaccen insha’i, abun so ne mai rubutu ya kiyaye wadannan abubuwa kamar haka:
- Kula da ka’idojin rubutun Hausa: Abu ne mai kyau a kula da ka’idojin rubutun Hausa a lokacin rubuta insha’i. Wato a rika dasa aya a gurin da ya ce, haka nan ma wakafi da sauran alamomin rubutu.
- Sassaukar Hausa: Amfani da Hausa mai saukin karantawa, yana da kyau sosai a fagen rubutu.
- Yin amfani da gajerun jimloli: Abu ne mai tarin fa’ida ya zamo mai rubutu ya yi amfani da gajerun jimloli a cikin rubutunsa. Tsawaita jimla a wasu lokutan kan rikitar da mai karatu, musamman idan aka yi rashin sa’a ba a ajiye alamomin rubutun da suka da ce kuma a muhallan da suka da ce ba.
- Jeranta kalmomi: Jeranta kalmomi a nan na nufin a yi amfani da kalmar da ta dace, kuma a gurin da ya dace.
- Salo: Amfani da kyakkyawan salon rubutu kan taimaka wajen fito da hakikanin inda tunanin mai rubutu ya dosa. Abin so ne, ya zama an tsara rubutu daki-daki.
Rabe-Raben Insha’i
[gyara sashe | gyara masomin]- Insha’i na Labari.
- Insha’i na Muhawara.
- Insha’i na Bayani.
- Insha’i na wasiƙa.
Insha’i na Labari
[gyara sashe | gyara masomin]Shi ne insha’in da ake bayar da labarin faruwar wani abu a cikinsa. Wato a rubuta wani gajeren rubutu da ke baiwa mai karatu labarin wani abu da ya faru a baya. Wannan labarin kuma na iya zamowa gaskiya, ko kuma kirkirarre.
Insha’i na Muhawara
[gyara sashe | gyara masomin]Insha’i na muhawara shi ne insha’in da ake rubuta muhawara a ciki. Insha’i ne da mai rubuta shi ya ke faɗin ra’ayinsa dangane da wani abu a cikin rubutun, amma tare da hujjoji. Misali, mai rubutu yana iya cewa Noma ya fi Kiwo Amfani a Fannin Gona. To, sai kuma ya kawo dalilansa na faɗin wannan a cikin rubutun. Wannan shi ne insha’in muhawara.
Insha’i na Bayani
[gyara sashe | gyara masomin]Insha’i ne da mai rubuta shi ya ke yin bayani game da wani abu. Wannan bayani zai iya zamowa siffanta abun ake yi ta yadda da zarar mai karatu ya gama karanta wannan bayani, idan ya ga wannan abu zai iya gane shi, ko kuma bayani yake rubutawa game da yadda ake yin wani abu. Kamar a ce miyar kuka ga misali. Koma dai me aka dauka, a cikin insha’in bayani ana rubuta cikakken, gamsasshen bayani ne game da wani abu.
Insha’i na Wasika
[gyara sashe | gyara masomin]Insha’i ne da mai rubutu ke rubuta labari, ko bayani a cikin tsarin wasika.
Ya zuwa wannan gaba, mai karatu zai fahimci cewa insha’i shi ne wani gajeren rubutu wanda ka iya zama labari, muhawara, bayani, ko kuma wasika. Sannan kuma gabatarwa, gundarin jawabi, da kammalawa su ke haɗuwa su samar da insha’i. Idan mai rubutu ya yi amfani da ka’idojin rubutu, ya jejjera kalmomin da suka dace a kuma gurin da suka dace, sannan kuma a cikin gajerun jimloli, kuma a cikin sakin layi, sakin layi, kuma ya yi amfani da Hausa mai sauki, to, ba makawa zai rubuta insha’i mai kyau.
Manazarta:
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.