Jump to content

Isa Bello Ja

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Isa Bello Ja (Dattijo Arziki) Jarumi ne sannan kuma dattijo a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ya Dade Yana fim a masana'antar, a matsayin ubsyake a gurin Yan fim , kyakkyawan bafullatani ne tsoho , Ya fito a fim Mai dogon zango na Tashar arewa 24 Mai suna DADIN KOWA, inda ya fito a suna alkali dikku.Mawaki Alan Waka yai masa Waka ta musamman.[1]wakar dattijon arziki.

Takaitaccen Tarihin Sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Isa bello ja dattijon arziki, ya samo wannan sunan ne daga matasa a masana'antar fim suka sa masa bisa ga sunan ya cancanta dashi saboda kamewarsa be fim din da zai zubar masa da mutunci. Jarumi ne na dattawan masana'antar sanann Dan siyasa ne. [2]Yayi karatun firamare da sakandiri Dana isalama a garin Kano [3]kasancewar sa malamin addini yasa ake ce masa dattijon arziki ya fara fim shekaru 44 tun kafin kafuwar kanniwud. Yana da mata daya da Yara goma Sha daya takwas Maza uku mata[4]. Yayi fina finai da dama a masana'antar kamar fim din fati yar Adamawa , dadin KOWA da saura da dama.[5]

  1. https://m.youtube.com/watch?v=okoX0-83z4w
  2. http://hausafilms.tv/actor/isa_bello_ja
  3. https://www.bbc.com/hausa/media-61015710
  4. https://m.youtube.com/watch?v=c2e1aBTG_z0
  5. https://www.blueprint.ng/why-i-choose-the-roles-i-act-by-isa-bello-ja/