Isabel Fernandes

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Isabel Fernandes
Rayuwa
Haihuwa 5 ga Yuni, 1985 (38 shekaru)
ƙasa Angola
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a handball player (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru GP G
Atlético Petróleos de Luanda (en) Fassara-
 

Isabel Sambovo Fernandes, a.k.a. Belezura (an haife ta a ranar 5 ga watan Yuni 1985) tsohuwar 'yar wasan ƙwallon hannu ce daga Angola.[1] Ta kasance memba a kungiyar kwallon hannu ta mata ta Angola, kuma ta halarci gasar kwallon hannu ta mata ta duniya a shekarar 2011 a Brazil da kuma wasannin Olympics na bazara a shekarun 2004, 2008 da kuma 2012.[2]

Belezura ita ce zakarar Afirka sau 5, bayan da ta lashe irin wadannan kambun a shekarun 2004, 2006, 2008, 2010 da 2012.

Belezura ita ce ta fi zura kwallaye a Gasar Ƙwallon hannu ta Ƙwararrun Mata ta Duniya ta shekarar 2005.

A karshe ta buga wasan ƙwallon hannu a kungiyar kasar Angola Petro Atlético.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Jerin 'yan wasan kwallon hannu na kasa da kasa na Angola

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill ; et al. " Isabel Fernandes Olympic Results" . Olympics at Sports-Reference.com . Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 13 August 2017.
  2. "XX Women's World Handball Championship 2011; Brasil – Team Roaster Angola" (PDF). International Handball Federation . Retrieved 5 December 2011.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

Isabel Fernandes at Olympics.com

Isabel Fernandes at Olympedia