Iska

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Iska
gas, mixture, chemical substance
subclass ofgas, mixture Gyara
uselifting gas, combustion Gyara
jirgi
Iska ce ke taimakawa jirgin sama tashi a sararin samaniya

Iska wani irin sinadari ne wadda Allah ya halitta, wanda ya watsa ta a cikin sararin duniya tun daga kasa har zuwa sararin samaniya. Sinadarin dake kunshe cikin iska shi yake taimakawa duk wata halitta samun damar rayuwa, babu wata halitta da zata iya rayuwa ba tare da iska ba. Sinadarin iska Dan Adam bazai iya gani da ido ba, ko kamawa da hannu ko dandanawa da harshe, sai dai ya shaka da hanci wanda amfanin iskar kenan dama ga duk wata halitta. Dan Adam bazai iya rayuwa tsawon minti biyar ba batare da iska ba. Acikin duniyan nan tamu ce kadai zaka iya samun iska, amma idan ka haura zuwa wasu duniyoyi kamar duniyar wata bazaka tarar da iska ba, dan haka ƴan sama jannati wato (astronomers) suke goya wadansu irin akwati mai dauke da iska aciki, wadda zai taimaka musu samun damar numfasawa yayin da suka fice daga wannan duniyar tamu. Wadda ba dan haka ba to da bazai yiwu su rayu ba. Iska ana iya jinta a jiki yayin data kada, kwayoyin halittar dake cikin fata masu isar da sako zuwa ga ƙwaƙwalwa sune ke sanya mutum yaji iska ajikinsa me sanyi ce ko me zafi, nan take zasu isar da sakon ga ƙwaƙwalwa ita kuma sai tayi tankade da rairaya ta fassara yanayin a jiki.