Jump to content

Itchan Kala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Itchan Kala


Wuri
Map
 41°22′40″N 60°21′34″E / 41.377718°N 60.359476°E / 41.377718; 60.359476
Ƴantacciyar ƙasaUzbekistan
Region of Uzbekistan (en) FassaraXorazm Region (en) Fassara
BirniKhiva (en) Fassara
Labarin ƙasa
Yawan fili 37.5 ha
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+05:00 (en) Fassara
hoton wani wuri a birmin itchrn kala

Ichan Kala (Uzbek: Ichan-Qаl'а) birni ne na ciki mai katanga na birnin Khiva, Uzbekistan. Tun a shekarar 1990 aka tabbatar da shi a matsayin Gidan Tarihi na Duniya.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Tsohon garin yana dauke da abubuwan tarihi sama da 50 da tsoffin gidaje 250, tun daga ƙarni na sha takwas ko na sha tara. Masallacin Djuma, alal misali, an kafa shi a karni na goma kuma an sake gina shi daga 1788 zuwa 1789, kodayake zauren gidan da aka yi bikinsa yana da ginshiƙai 112 da aka ɗauka daga tsoffin gine-gine.

Fasali[gyara sashe | gyara masomin]

Mafi kyawun fasali na Ichan Kala shi ne bangon bulo mai ƙyalli da kofofi huɗu, ɗaya a kowane gefen kagara mai kusurwa huɗu. Kodayake ana jin an aza harsashin ne a ƙarni na goma, a yau an gina katanga mai tsayin mita 10 (33 ft) galibi a ƙarshen karni na sha bakwai kuma daga baya aka gyara su.

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]