Jump to content

Jacob Kwame

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

ASARE, Jacob Kwame BSc, LLB (Hons), an haifeshi ranar 29 ga watan Satumba, 1929 a Oda dake Ghana. Lauya ne ɗan Ghana, kuma injiniyan lantarki

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara Makarantar Gwamnati Oda a shekaran 1934-43, Kwalejin Jami'a, Ghana, 1949-51, Jami'ar Southampton, Ingila, 1951-54, Jami'ar Ghana, 1967-70; darektan Injiniya, Gidan Watsa Labarai na Ghana, 1968-71, Mataimakin Manajan Darakta na Kamfanin Masana'antu na Ghana (GIHOC), 1971-84, mai ritaya, 1984, an kuma naɗa shi babban darakta, Cibiyar Horar da Sake Bincike ta Afirka, 1984; ɗan'uwa, Ghana Institution of Electri-cal Engineers, shugaba tun 1975, memba, Institution of Electrical Engineers, United Kingdom

ya auri Grace Faustina Ama Assoku a shekaran 1965 wanda kuma yaran su hudu sune kuma mace daya sai maza uku.[1]

  1. Africa who's who (2nd ed ed.). London: Africa Books Ltd. 1991. ISBN 0-903274-17-5. OCLC 24954393. Empty citation (help): p.p,324.381|edition= has extra text (help)