Jacqueline Maria Duarte Pires Ferreira Pires

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Jaqueline Maria Duarte Pires Ferreira Rodrigues Pires (an haife ta a ranar 1 ga watan Nuwamba, 1968) 'yar diflomasiya ce ta Cape Verde. Daga shekarun 2015 zuwa 2019, ta kasance Jakadiya a Jamus. [1] [2]

Ta kammala karatu daga Jami'ar Lisbon, da Jami'ar Katolika ta Portugal. [1] A shekarar 1995, ta kasance sakatariyar jakadanci. Daga shekarun 1998 zuwa 2001 ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara da Majalisar Ɗinkin Duniya. A shekarar 2001, ta zama mai ba da shawara ga Ministan Harkokin Wajen Cape Verde. Daga shekarun 2004 zuwa 2009, ta kasance mai ba da shawara ga Babban Sakatare na Ƙungiyar Ƙasashen Harshen Portuguese. Daga shekarar 2010 zuwa 2012, ta kasance mataimakiyar daraktar harkokin siyasa da haɗin gwiwa ta ƙasa a ma'aikatar harkokin wajen Cape Verde. Daga shekarun 2012 zuwa 2015, ta kasance mai ba da shawara ta diflomasiyya ga Firayim Minista.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Former Ambassadors in Germany". diplomatisches-magazin.de (in Turanci). Retrieved 2021-02-16. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. "Cape Verde". www.berlinglobal.org (in Turanci). Retrieved 2021-02-16.