Jump to content

Jacques Nziza

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jacques Nziza
Rayuwa
Sana'a
Sana'a soja

Manjo Janar Jack Nziza shi ne Sufeto-Janar na Rundunar Tsaro ta Ruwanda.[1] Hakazalika ya yi aiki a matsayin babban sakataren ma'aikatar tsaro.

André Kissasse Ngandu [fr], wanda ya kafa AFDL, kawancen da zai kawo karshen Mobutu Sese Seko a matsayin shugaban kasar Zaire a 1997, an kashe shi a ranar 6 ga watan Janairun 1997. Rashin jituwa tsakanin shugabannin AFDL ya kai ga kisan. Wata majiya ta kusa da Ngandu ta ambaci Nziza a matsayin wanda ya aikata kisan, wanda shugaban AFDL Laurent-Désiré Kabila ya bada Umarni.[2]

  1. "Former UN Mission Chief Appointed As New RDF Chief Of Defence Staff". News of Rwanda. 23 June 2013.
  2. Filip Reyntjens (24 August 2009). The Great African War: Congo and Regional Geopolitics, 1996-2006. Cambridge University Press. pp. 107–108. ISBN 978-0-521-11128-7.

Hanyoyin hadi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]