Jump to content

Jessie Buckley

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Jessie Buckley an haife ta a watan Disamba na shekara ta 1989 yar wasan kwaikwayo ce kuma mawakiya yar kasar Irish. Kyaututtuka da ta samu sun hada da lambar yabo ta Laurence Olivier, sannan kuma tana cikin jerin wadanda sunan su ke cikin lambar yabo ta Academy Award sai kyaututukan BAFTA guda uku.

Buckley ta fara aikinta a shekara ta 2008 a matsayin mai takara a wasan kwaikwayo na BBc TV, inda ta zo ta biyu. Ta kammala karatun RADA, bayyanarta ta farko a cikin jerin shirye-shiryen talabijin na BBC, kamar War & Peace (2016) da kuma shirin Taboo (2017). Buckley ta fara fim dinta tana taka rawa a Beast (2017), kuma ta sami ci gaba a fim din Wild Rose (2018). Jajircewar ta da tayi wajen waka yasa aka ayyana sunanta a cikin jerin wadanda zasu iya lashe gasar BAFTA Award.

Rayuwar ta da Karatun ta

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Buckley a watan Disamba na shekara ta 1989 a cikin garin Killarney, da Marina Cassidy da Tim Buckley [1]Buckley nada karamin kani da kuma kanne mata guda ukku.[2]


"Jessie Buckley's dad on her 'wonderful' Oscar nod". Rte.ie. 9 February 2022. Archived from the original on 8 March 2022. Retrieved 4 March 2022.

  1. "Jessie Buckley's dad on her 'wonderful' Oscar nod". 9 February 2022. Archived from the original on 8 March 2022. Retrieved 4 March 2022. Cite journal requires |journal= (help)
  2. Murphy, Greg (9 February 2022). "Who is Jessie Buckley? Kerry star gets first Oscar nod for 'The Lost Daughter'". Irish Examiner (in Turanci). Archived from the original on 4 September 2022. Retrieved 4 September 2022.