Jump to content

Ka'idojin rubutun hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

kA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA Kamar yadda aka sani, kowanne lamari na duniya yana da ka'idar yadda ya kamata a gudanar da shi. Kuma bin ka'idar ita ke sa a sami dacen yadda ake bukata ba tare da an fuskanci wata matsala ba. Idan kuma ba a bi ka'idar ba a ga ba daidai ba. Tunda yake haka ne, rubutun Hausa shi ma, yana da ka'idarsa. Bin ka'idojin rubutun Hausa sau-da-kafa, su ke sa a sami rubutu mai Cikakkiyar ma'ana. Wato a sami daidaiton manufa tsakanin tunanain marubuci da kuma na makaranci.

ABUNDA AKE NUFI DA KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA[gyara sashe | gyara masomin]

Ka'idojin rubutun Hausa, wani yanayi ne na lura da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai da daidai, ba tare da canzawar ma'anar da marubuci ke nufi ba . Haka kuma, yana samar da saukin fahimtar karatu daga mai karantawa.


FANNONIN KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA[gyara sashe | gyara masomin]

Fannonin ka'idojin rubutun Hausa da muke da su a nan, suna da dama. Kuma sune ginshin duk abinda ya kamata marubuci ya koya game da ka'idojin rubutun Hausa domin samun gwanancewa a rubutu. Don haka, zan zayyano su, sannan kuma na yi bayaninsu daki-daki kamar haka:

1- Alamomin ajiye magana; 2- Raba kalma da kuma hade kalma; 3- Yarda ake amfani da shaddatun bakaken Hausa; 4- Gajera da doguwar mallaka; 5- Dafa-keya 'w' da jakada 'w'; 6- Daurin 'm' da daurin 'n'; 7- 1.0 ALAMOMIN AJIYE MAGANA (punctuation mark)

  Ga alamomin aje magana magana tare da bayanansu daki-daki:

1.1 Aya [.] Ita aya almar dugo ce, wace ake saka wa a cikin rbutu. Aya tana zuwa ne a karshen jimla, a lokacin da magana ta cika, sai a sami cikakiyar tsayawa a yayin karatu ko magana. Missali:

** A ranar da aka rantsar da sabon Shugaban kasar Najeriya Ahmad Bola Tunubu, ya ayyana janye tallafin man fetur. Sannan kuma, ya cigaba ba da zayyana wasu manufofin Gwamnatin tashi.** 

idan an lura za a ga an sami ayoyi goda biyu a cikin missalin da na kawo. Wato daya a takiya daya a karshe. Amma duk da haka, ai kokarin tartan tantancewa domin wakafi ma, ya zo sau biyu a ciki. Idan an yi hattara sosai, shi ma sai ai la'akari da shi a missalin wakafi da zai zo nan gaba kadan.

1.2 Wakafi [,]

  Wakafi, wata karmar tsayawa ce, wato dakatawa ko tsahirtawa wacce ba kai ta aya ba. Missali:
  "Na ga wani farin mutum jiya, sanye da faren kaya da jar hula, yana tsallaka titi a natse"

To a nan, za a ga an yi amfani da wakafi guda uku kafin aya da ta zo a karshe. Bayan hakka, ana samin wakafi yayin da ake zayyana wasu abubuwa. Missali:

    • Wani Attajiri, ya rabawa mabukata kayan abinci kyauta a garin Gogori. Irin su shinkafa, masara, gero, wake, manja,sukari da sauransu.**

A wannan missalin za a ga yadda ake saka wakafi a tsakankanin abubuwan da aka raba. Wato shinkafa da masara da dawa, har zuwa karshe.

1.3 Ayar tambay [?] Ita almar ayar tambaya, alama ce da take fayyace jimlar da ke kunshe da tabaya. A yayain da marubuci yai nufin tambaya a cikin rubutunsa kuma bai sa wannan alama ba (?) To wannan jimla za ta tsaya ne a matsayin bayani maimakon tambya. Kuma, babu bukatar amsa domin ba a sa almar tambaya ba.Missali:

 Aliyu ya zo?, 
 menene ake sayarwa?

Idan aka yi lam'akari missalan da ke sama, za a ga an kawo jimloli guda biyu kuma dukkanin suna dauke da alamar tambaya. Bayan haka, a duba kasa za a ga an sake maimaita jimlar farko ba tare da alamar tambaya ba:

 Aliyu ya zo

A nan za a fahimci cewa ana yin bayanin cewa Aliyu ya riga har ya zo wani wuri ne, maimakon tambaya akan zuwan Aliyu wani wuri.

1.4 Aya mai ruwa/ Ruwa biyu [:] Wannan wata alama ce da ta ke alamata nuni da zuwan wasu abubuwa a kasa, haka kuma ana amfani da su waje fayyace awanni, minting da kuma sakanni na lokaci. Missal:

 A= 12:56 (wato karfe sha biyu da minti hamsin da shida)
 B= Missali na biyu a duba duk inda na ce MISSALI za a ga na yi wannan alamar [:] 
    sannan a ga missalan sun biyo baya. To wannan ma na daya daga cikin amfanita
 C= idan an zo zayyana wasu abubuwa, akan yi amfani da wannan alama ta Ruwa-biyu. Kamar a ce, Shugaban kasa zayyana wasu manufofin Gwamnatinsa guda uku da tasa a gaba kamar haka;
  Inganta noma da kiwon dabbobi;
  Yaki da cin hanci da rashawa;
  Samar da isasshen man fetur; da sauransu. 

A nan idan aka lura sosai, za a ga sai da na sa alamar ruwa-biyu [:] sannan na kawo wadancan abubuwa uku da aka ce Shugaban kasa ya zayyana.

1.5 Wakafi mai ruwa [;] wannan alama ce da ake amfani da ita wajen raba jerin wasu jimloli ko kalmomi a cikin zance. Game da missali, a duba a missalin karshe na Aya mai ruwa , za a ga yadda aka bayyana abinda Shugaban kasa ya zayyana. A nan za a ga an sa Ka alamar (;) a gaban kowacce jimla. Ga Karin missali: A= Shugqban makarantar ya gargadi dalibai cewa,idan sun tashi dawowa daga hutu, su zo da kayan karatu kamar idan haka:

1 littafin koyon turanci, aji na biyar;
2 littafin koyan lissafi, aji na biyar;
3 littafin nazarin rayuwar dan Adam, aji na biyar;
4 littafin koyan karatn Hausa, aji na biyar.

A wadannan missalai za a lura cewa, a duk karshen jimloli 3 na farko an saka alamaar tsayawa ta wakafi mai ruwa (;), in banda jimla ta karshe da aka yi wa alamar aya (.)

1.6 Alamar Zarce [-] Zarce, alama ce da ake amfani da ita wajen hade kalmomi biyu ko sama da biyu, su zama kalma daya da ma'ana daya. Akan saga wannan alama a takanin kalmomi da suka zo iri daya ko wadanda suka zo daban-daban. Kin saka wannan alama a inda ya dace, yakan kawo sabanin ma'ana. Missali:

1 malam-buda-mana-littafi (sunnan wani kafilfilo);
2 fadi-ka-mutu (tangaran);
3 fari-fari (abinda bai kai fari sosai ba);
4 malfar-ungulu (wani tsiro ne); dss.

A lura da kyau, idan muaka dauki missali na farko, (malam-buda-mana-littafi) za mu ga yana nufin sunan wani abu wato, kafilfilo. Idan kuma ba a sa wannan alama ba a tsakankanin kalmomin (malam buda mana littafi) to rubutun ya zama wata jimla mai nufin umarni. Wato, dalibai ne ke umartar malaminsu da ya buda masu littafi.

1.7 Alamar zancen wani [" "].Wannan alama ce da marubuci yake amfani da ita wajen nuna maganar wani mutun kai-tsaye. Wato a nan mawallafi ko marubuci zai Bude maganar wani ta kai-tsaye da wannan alamar ["], sannan idan magaanr ta zo karshe sai ya rufe da irin wannan alamar ["]. Ga missqli kamar haka:

1 A yayin da 'yanjaridu suke ganawa da shugaban kasar, ya dau alkawari na inganta rayuwar al'ummar kasar tashi. Har ma yake cewa: "Ya ku al'ummar wannan kasa tamu mai cike da albarka. Ina yi maku albishir da cewa, daga yau na sauke farshin man fetur da kaso hamsin cikin dari (50%). Bayan haka kuma, zan raba wa Manoma takin zamani da sauran kayan aikin gona kyauta domin farfado da tattalin arzikin kasar nan".
 A wannan dan missali da ke sama, za mu fahimci yadda aka bayyana jawabin Shugaban kasa kai tsaye.

1.8 Alamar baka-biyu ( ). Wannan wata alama ce da ake amfani da ita wajen nuna karin bayani akan wata kalma ko a kan wani abu.