Jump to content

Kabilar Egbema

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kabilar Egbema da ake kira daular Egbema, na ƙabilar Ijaw na zaune a jihohin Delta da Edo. Masarautar ta rabu a siyasance zuwa jihohi biyu daban-daban saboda ƙirƙiro jihohin Najeriya.

Egbema suna da muhimman al'adun Ijaw, duk da kasancewarsu a yammacin kasar Ijaw, Masarautar ta samo asali ne daga ƙaura da dama daga yankin tsakiyar Ijaw ƙarni da suka wuce. Ƙabilar Egbema tana ƙarƙashin masarautar Agadagba na Masarautar Egbema. Masarautar ta ƙunshi ƙauyuka guda tara na asali (ƙaranoni) da ake kira Egbema-Isenabiri. Waɗannan su ne:[1]

  1. Ofiniama
  2. Ajakurama
  3. Opuama
  4. Ogbudugbudu
  5. Gbeoba
  6. Abere
  7. Abadigbene (Bolou-Jamagie)
  8. Jamaji, da kuma
  9. Ogbinbiri

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Monarch Urges FG To Merge Egbema Towns In Edo, Delta". Vanguard News (in Turanci). 2019-03-24. Retrieved 2021-09-10.