Jump to content

Kabiru Hassan Dashi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hon. Kabiru Hassan Dashi (An haifeshi ranar 2 ga watan Yunin shekarar 1976) a garin Dashi da ke a ƙaramar hukumar Kabiru Hassan

Kabiru Hassan

Honorabul Kabiru Hassan Dashi ya halarci makarantar firamare ta Dashi daga shekarar 1989- shekarar 1988 da JSS, Galadimawa a shekarar 1989 a karamar makarantar sa. Ya wuce babbar Sakandare a GSS Kafin Maiyaki a shekarar 1992..Yayi karatu na Higher National Diploma (HND) akan Accounting and Finance da Post Graduate Diploma in Accounting and Finance.a BUK. [1]

An zabi Dashi a matsayin mai ba da shawara a unguwar Dashi kuma ya kuma zama shugaban kansila. Daga nan kuma aka nada shi a matsayin Sakataren Majalisar Kananan Hukumomi, (Monitor State CRC ) da Shugaban Matasan Karamar Hukumar PDP.

Yana aiki da ma'aikatar kananan hukumomi ta jiha a matsayin akawu daga shekarar 2008-2014. Da radin kansa ya ajiye mukaminsa na tsayawa takarar majalisar dokokin jihar Kano a shekarar 2015 inda ya samu nasara a karkashin jam’iyyar APC. Sannan kuma ya kara lashe zabensa karo na biyu a shekarar 2019 kuma yasamu mukamin Majority leader 2019-2020.[2]

A ranar 15 ga watan Disamba, 2020 ya sauka daga muƙaminsa na shugaban masu rinjaye na majalisar kuma aka maye gurbinsa da Hon. Labaran Abdul Madari. [3]

  1. https://www.thisdaylive.com/index.php/2020/12/16/kano-house-of-assembly-elect-new-speaker-others
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-11-07. Retrieved 2021-11-07.
  3. https://dailynigerian.com/tag/kabiru-dashi